22 Janairu 2022 - 12:50
An Rufe Makarantu A Aljeriya Saboda Yaduwar Cutar Korona

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar Aljeriya Tebboune ya bukaci a rufe dukkan makarantu a fadin kasar na tsawon kwanaki 10. Wannan matakin yazo ne bayan taron gaggawa da yayi da majalisar ministocinsa da kuma kumitin yaki da cutar korona a kasar

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tun daga ranar Alhamis ce aka rufe dukkan makarantu a fadin kasar saboda yadda cutar Koron Nau’in Delta da Omicron da take yaduwa cikin sauri kamar wutar daci a kasar.

Jami’an lafiya a kasar sun fitar da sanarwa cewa kiddidigar da aka fitar ta nuna cewa kimanin mutane 1359 aka tabatar da sun kamu da cutar Omicron a fadin kasar inda 12 daga cikinsu ma sun mutu,

Daga karshe shugaban kasar y ace jami’an kiwon lafiya da ma’ailatan Jami’oi su ne ked a Alhakin duba yi yuwar ci gaba da zuwa aiki ko kuma tsarin day a dace su bi.

342/