Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Hukumar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da Babban Kwamishina kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Ilmantar da Masu Zaɓe na hukumar, Mista Festus Okoye, ya fitar.
Okoye ya ce an yanke shawarar hakan ne a wajen taron mako-mako da INEC ke yi da kuma wani taro na musamman da aka gudanar a ranar Juma’a inda aka tattauna kan al’amuran da su ka janyo samuwar guraben da za a cike da saka ranar zaɓuɓɓukan da kuma yanayin tsaro a wasu daga cikin jihohin da abin ya shafa.
Okoye ya ce an yanke shawarar ne bayan da kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya, da kakakin Majalisun Dokoki na wasu daga cikin jihohin su ka bayyana samuwar guraben.
342/