Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Labarin ya kara da cewa a ranar 8 ga watan Jenerun da muke ciki ma sojojin kasar ta Syriya sun hana wata Tawagar sojojin Amurka wucewa a yankin Arewa maso yammacin lardin na Hasaka.
Amurka ta mamaye arewacin kasar Siriya ne a shekara ta 2014 da sunan yaki da ISIS ko Deash, amma a halin yanzu ta kafa sansanonin sojojinta har guda 28 a kusa da rijiyoyin man fetur dake yankin suna satar man kasar suna kuma taimakwa wata kungiyar ‘yan ta’adda wacce ake kira KASAD da kudaden man da take haka a yankin don ta ci gaba da yakar sojojin Syriya.
342/