Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - An gudanar da irin wannan taro a birnin Bagadaza fadar mulkin kasar ta Iraki, inda mutane kimanin miliyan uku suka halarci gangamin, wanda ba a taba ganin makamancinsa a birnin ba. Babban kwanadan dakarun sa kai na kasar Iraki Faleh Fayyad ya gabatar da jawabia wurin, inda ya jaddada wajabcin ficewar sojojin Amurka daga kasar Iraki a daidai wa'adin da aka diba musu, inda ya ce babu wani sassauci kan wanna matsayar da al'ummar Iraki suka dauka. Baya ga birnin Bagadaza, an gudanar da irin wannan gangamia wasu biranen, da suka hada da Najaf, Karbala da sauransu, inda malamai da jami'ai da sauran dubban al'ummar gari suka halarta. Amurka ta kashe Kasim Sulaimani tare da Abu Mahdi Muhandis ne a ranar 1 ga watan Janairun 2020, bayan da shugaban Amurka na lokacin Donald Trump ya bayar da umarnin yin hakan.
342/