31 Disamba 2021 - 13:13
​Afrika Ta Kudu : An Fara Ban Kwana Da Gawar Desmond Tutu

A Afrika ta Kudu, an fara ban kwana da gawar mirigayi Archbishop Desmond Tutu, wanda ya rasu ranar Lahadi da ta gabata.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - An kai gawar marigayi ne a cocin St George's Cathedral da ke Cape Town a a wannan Alhamis inda za ta kwashe kwana biyu domin mutane su yi ban kwana da ita.

A hukumance za a yi jana'izarsa ranar Asabar 1 ga watan Janairu bayan mutane sun gama ban kwana da gawarsa, sannan za a kona gawarsa a kuma ajiye tokar a cikin cocin, inda ya kwashe shekaru da dama yana wa'azi.

Desmond Tutu wanda ake matukar mutuntawa, wanda ya kasance a sawun gaba wajen yaki da gwamnatin wariyar launin fata, ya taba samun lambar yabo ta nobel kan zaman lafiya.

342/