Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ziyarar tana zuwa ne bayan goron gayyata da shugaban kasar Rasha Biladmir Putin ya aikewa da shugaba Ra’isi , kuma ana sa ran za su tattauna game da muhimman batutuwa da suka shafi kasa da kasa da kuma yadda kasahen biyu za su ci gajiyar juna a bangarorin tattalin arziki da cinikayya .
Da yake bayani game da ranar 30 ga watan Disemba kuma ya fadi cewa “Rana ce da Alummar Iran suka wargaza makircin Amurka na kawo rarrabuwar kai a kasar, dubun dubatan alummar kasa ne ke fitowa kan tituna a manyan biranen kasar a irin wannan rana domin yin tir da yunkurin da Amurka ta yi na haifar da rashin tsaro da tarzoma a lokacin zaben shugaban kasa na shekara ta 2009 da aka yi a kasar iran.
342/