Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Jaridar Leadership ta Najeriya ta bayyana cewa a halin yanzu mutane kimani 520,670 suke jiran a yi masu alluran zagaye na biyu , amma duk inda suka je sai a ce masu babu ita.
Jaridar Leadership ta zagaya wasu cibiyoyin alluran a cikin jihar ta kuma tabbatar da cewa babu ita. Ya zuwa yanzu dai an yi wa mutane 950,067 alluran riga kafin cutar samfurin Astra Zaneka, sannan daga cikin wannan adadin muatne 511,003 ne suka sami yin na biyu.
Sai kuma samfurin Modema inda mutane 317,784 suka sami yin na farko sannan wasu 236,178 kuma suka yi na biyu. Wasu mutanen birnin Logas sun bayyana cewa an yi makonni biyu kenan suna ta kai kawo tsakanin cibiyoyin alluran ba tare da an yi masu ba, saboda karancinsu.
342/