Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - shugaban ya fada a wata sanarwa cewa firaministan ya kasa sauke yaunin dake wuyansa na shirya zabe kamar yadda yarjejeniyar 17 ga watan Satumban 2020 ta tanada.
Tuni shugaban kasar ya kira wani taron tuntuba da zai hada gwamnatin tarayya, da hukumomin yankunan Somalia, da kuma hukumomin Mogadisho, domin zabar wani tsari da zai kai ga shirya zabubuwa, da suka hada da na wakilai na majakisar koli da ta dokoki da kuma na shugaban kasa.
Matakin dai ya zo ‘yan sa’o’I bayan korar shugaban hukumar zaben kasar .
342/