25 Disamba 2021 - 14:13
Iran: Ra'isi Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Zagayowar Ranar Haihuwar Annabi Isa (AS)

Acikin sakon taya murna da shugaban kasar Iran Ibrahim Ra’isi ya aikewa da mabiya Addinin kirista na duniya na murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Isa (As), yace : Annabi ne da ya yi kira zuwa ga zaman lafiya da alheri, kuma damace ta nuna kauna da yan uwantaka da dukkan’ ya’yan Adam.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Haihuwar Annabi Isa ( As) ya nuna karfin kudurar Ubangiji da kuma matsayin sayyadatuna Maryam mahaifiyar Annabi Isa (As) da kuma girman matsayin da mace take da shi a addinan da aka saukar daga sama, idan aka tuna lokacin da Mala’ika ya zo mata yace: “ ya maryam hakika Allah ya tsarkakeki kuma ya zabe ki daga cikin matan duniya.

Yace yin bukin tunawa da zagayowar wannan rana wata damace na karrama sayyidatuna maryam (As) kuma lokaci ne na tunawa da koyi da kyawawan halaye na Annabi Isa As, da kuma fada da zalunci da yayi da cusa fata na gari ga raunana domin samun makoma ta gari .

342/