25 Disamba 2021 - 13:50
Abdullahiyan: Atisayin ‘Rasulul Azam 17’ Sakon ‘Yan Uwantaka Ne Ga Kasashen Makwobta

Ministan harkokin wajen kasar Iran Husain Amir Abdullahiyan ya ce atisayen ‘Rasulul Azam 17’ wanda aka gudanar a yankin Tekun Farisa da mashigar ruwa ta Hurmuz, duk tare da cewa sako ne babba ga wadanda suke son kawo matsalolin a cikin harkokin tsaron kasar Iran, amma a lokaci guda sako ne na 'yan'uwantaka ga dukkan kasashe kawaye ga kasar Iran da kuma makobta.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A ranar litinin da ya gabata ce hadin Giwan sojojin kasar Iran, na sama da kasa da kuma ruwa suka gudanar da atisayen hadin giwa na kwanaki biyar a jere a cikin ruwan tekun farisa, mashigar ruwa ta Hurmuz da kuma wasu jihohin bakin ruwa daga kudancin kasar.

An gwada sabbin makamai da kuma nuna korewa a cikin ayyukan tsaron kadar daga mikiya, wadanda suka bayyana adawa da kasar. Sai dai itisayen ba barazana bace ga dukkan makobtan kasar Iran.

342/