Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA – ya habarta cewa, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya sanar da rasuwar jakadan Iran da ke kasar Yemen sakamakon kamuwa da ciwon Korona.
Malam Haj Hassan Hassan Irloo, wanda ya kasance cikin aiki bangare sinadarai , ya kamu da cutar korona a wurin aikin sa, kuma abin takaici ya dawo kasar cikin yanayi mara dadi.
Sai dai kuma abin takaicin shi ne, duk da cewa ya yi amfani da dukkan hanyoyin magance cutar, ciwon nasa ya ci gaba har ta yadda wadannan matakan ba su taimaka ba, kuma wannan jami'in diflomasiyyar Iran ya yi bankwana da duniya a safiyar yau Talata 21 ga Disamba, 2021.
* Jana'izar
Za a fara jana'izar marigayin Haj Hassan Irloo da yammacin yau da karfe 3:45 na rana a ma'aikatar harkokin wajen kasar.
342/