Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Ana atisayen ne a tekun farisa da mashigar Hormuz da gabar ruwan Hormozgan, Bushehr da lardunan Khuzestan.
Mataimakin babban jami’in gudanarwa na IRGC, kuma mai magana da yawun atisayen Birgediya Janar Abass Nilforoushan ya sanar da fara atisayen na tsawon kwanaki biyar.
Atisayen ya yada dakarun rukunonin dakarun rindinar na sama da kasa dana sararin samaniya da kuma dakarun sa kai na Basij, a wani mataki na dakile barazanar da ake gani daga makiya.
342/