Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - A yau Litini, Antonio Guteress zai jagoranci wani taro tare da fira ministan Lebanon, da zai samu halartar wakilan kungiyoyin MDD dake Lebanon, a wani mataki na hada karfi da karfe domin taimakawa kasar ta Lebanon.
A ganawar da ya yi da shugaban Lebanon, babban sakataren na MDD, ya yaba da kokarin da Lebanon ta yi na karbar ‘yan gudun hijirar Siriya, duk da tarin matsalolin tabarbarewar tattalin arziki da take fama dasu.
Ya kuma jadadda anniyar MDD, na taimakawa Lebanon da al’ummarta, ta hanyar tuntuba da tattaunawa da dukkan bangarori domin kawo karshen halin da aka shiga a Lebanon.
342/