13 Disamba 2021 - 14:03
Shugabanin ECOWAS Na Taron Kungiyar Karo Na 60 A Abuja

Shugabannin kasashe da na gwamnatocin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS, na halrtar taronsu karo na 60 a Abuja fadar mulkin Najeriya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Taron zai maida hankali kan wasu sauye sauye na karfafa ayyukan kungiyar, dama wasu batutuwa da suka shafi tsaro, tattalin arziki da kuma siyasa a yankin.

Haka kuma shugabanin zasu duba halin da ake ciki a kasashen Mali da Guinea da sojoji ke rike da mulki.

342/