13 Disamba 2021 - 14:02
Iran Ta Taya Kenya Murnar Zagayowar Ranar Samun ‘Yanci

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta taya kasar Kenya da al’ummarta murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kai, a yayin da kasar ke bikin cika shakaru 58 da samun ‘yancin kai.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - A wani sako da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, ta fitar ta ce tana taya Kenya daya daga cikin manyan abokanta a Afrika ta fuskar alakar tattalin arziki murna game da zagayowar wannan rana.

A Yau Lahadi ne al’ummar kasar Kenya ke gudanar da bukukuwan cika shekaru 58 da samun ‘yancin kai daga mulkin Mallaka na turawan Ingila.

Kenya dai ta kasance a karkashin mulkin mallakar kasar Ingila tun daga shekarar 1895 har zuwa ranar 12 ga watan Disamba na 1963.

342/