Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - An tsara firaministan na Isra’ila zai gana da yarima mai jiran gado na Abou Dhabi cheikh Mohammed ben Zayed Al-Nahyane.
Bangarorin biyu zasu tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi yankin da kuma karfafa alaka a tsakaninsu a cewar ofishin firaministan Isra’ilar.
Ziyarar dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake cikin tattaunawar Vienna da nufin farfado da yarjejeniyar nukiliyar da manyan kasashen duniya suka cimma da Iran a 2015.
Isra’ila dai na ci gaba da sukan tattaunawar, inda kuma ta bukaci Amurka data janye jiki daga tattaunawar tare da daukar matakai masu nagarta kan Iran.
342/