8 Disamba 2021 - 13:11
Covid-19 : Afrika Na Kimsa Samar Da Rigakafinta

Cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Afirka (Africa CDC) ta gudanar da wani babban taro na hadin gwiwar samar da allurar rigakafin cutar korrona a Kigali, babban birnin kasar Rwanda.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- Mahalarta taron sun yi imanin cewa, saboda rashin adalci game da rarraba allurar rigakafi da wasu dalilai, ya zama wajibi a kara karfin samar da rigakafin a Afirka.

Manufar taron na kwanaki biyu, ita ce kara tattaunawa kan ci gaban samar da rigakafin.

Babban darektan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana a taron cewa, sama da kashi 18 cikin 100 na sabbin alluran rigakafin COVID-19 suna zuwa kasashen mafiya karfin tattalin arziki na G20 ne, yayin da kasashe masu karamin karfi ke samun kashi 0.6 cikin 100 na allurar rigakafi a duniya.

Rashin adalci dangane da rabon alluran rigakafin na COVID-19, da bullar nau’in cutar na Omicron, ya nuna muhimmancin inganta karfin samar da allurar rigakafi a Afirka.

342/