7 Disamba 2021 - 14:43
An sake Zabar Adama Barrow A Matsayin Shugaban Kasar Gambia

Hukumar zaben kasar Gambia, ta ayyana Adama Barrow, a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar da aka gudnar a ranar Asabar.

Yayin da yake sanar da shugaban hukumar ta IEC, Alieu Momar, ya ce Adama Barrow, jagoran jam’iyyar NPP, shi ne wanda ya lashe zaben shugaban kasar.

M. Barrow ya samu jimillar kuri’u dubu 457 da 519, kwatankwacin kashi 53 bisa 100 na yawan kuri’un da aka kada a zaben, Inda Ya yi galaba kan babban abokin takararsa Ousainu Darboe, na jam’iyyar UDP, wanda ya samu kuri’u dubu 238 da 253.

A shekarar 2016 aka zabi Barrow a karon farko a matsayin shugaban kasar Gambia karkashin hadakar kawancen jam’iyyun adawa bakwai har ma da ’yan takarar indifenda, inda ya kada tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh.

Tun daga wancan lokacin Jammeh yake gudun hijira a kasar Equatorial Guinea, bayan yak i amince shan kaye.