6 Disamba 2021 - 14:36
​Yemen: Mutane Akalla 30 ne Suka Rasa Rayukansu Ko Suka Ji Rauni Sanadiyyar Hare-Haren Jiragen Yakin Saudiya

A wasu mummunan hare-haren da jiragen yakin saudiya suka kai kan gidajen mutane a birnin San’aa babban birnin kasar Yemen a daren jiya Asabar akalla mutane fararen hula 30 ne suke rasa rayukansu ko suka ji rauni.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- kasar Iran ya kara da cewa mutane 16 suka rasa rayukansu a yayinsa wasu 16 kuma suka ji rauni a hare-haren jiragen saman yaki na kawancen Saudiya.

Labarin ya kara da cewa hare-haren na jiya sun shafi shagunan saida abinci da kuma gidajen mutane.

Tun cikin watan maris na shekara ta 2015 gwamnatin kasar Saudiya tare da kawayenta, wadanda suka hada da Amurka da kuma UAE suka farwa kasar Yemen da yaki suka kuma killace kasar ta Sama kasa da kuma ruwa, wanda ya jawo mutuwar dubban daruruwan mutane sannan wasu kimani miliyon 4 suka zama ‘yan gudan hijira.

Banda haka yakin ya lalata kasha 85% da manya-manyan ayyukan ci gaban kasar ya kuma jefata cikin yunwa da karancin abinci.

342/