4 Disamba 2021 - 14:54
MDD : Da’esh Ta Aikata Laifukan Yaki Da Cin Zarafin Dan Adam A Iraki

Wani rahoto da wasu masu bincike na MDD, suka gudanar ya nuna cewa kungiyar da’esh ta aikata laifukan yaki da cin zarafin bil adama a gidan yarin Mossul na Iraki a cikin watan Yuni 2014.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- Shugaban masu binciken, Christian Ritscher, ya bayyana a gaban kwamitin tsaron MDD, cewa binciken da sukayi a manyan kaburbura da aka binne fursunoni sun nuna yadda kungiyar ta azabtar da mutane a gidan yarin na Badush.

Fursunonin da aka cafke a lokacin an ware su aka kuma rarraba su bisa dogaro da addininsu, aka kuma ci zarafinsu, dag acikinsu kuma akwai ‘yan shia’a kimanin 1,000 da aka kashe.

A shekarar 2014, ne mayakan da’esh suka kwace biranen Iraki da dama, tare da ayyana Khalifa a wani yanki mai fadi na tsakanin Siriya da Iraki, a shekarar 2017 ne aka sanar da murkushe kungiyar a hukumance saidai har yanzu tana ci gaba da kai hare hare lokaci zuwa lokaci a Iraki.

342/