Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Khateeb zade ya yi kira ga dukkan bangarorin dake Tattaunawar da su yi watsi da duk wani abu da zai iya kawo cikas a ci gaba da tattaunawar da ake yi domin samun masalaha,
Shekaru 13 da suka gabata an cimma matsaya mai kyau a tattaunawar da ake yi kan shirin Nukiliyar iran, inda aka kammala komai a ranar 14 ga watan yulin shekara ta 2015, amma Donald Trumph na hawa mulki a shekara ta 2017 ya yi fatali da dukkan yarjejeniyar da aka cimma , a watan mayun shekara ta 2018 kuma ya sanar da ficewa daga ciki tare da sanya takunkumi mafi muni a tarihi kan kasar Iran,
Yanzu haka dai zaman na ci gaba da gudana a birnin Biyanna tsakanin wakilin iran da na kasashen turai 4 gami da kasar Jamus domin tattaunawa kan yadda za’a cire mata takunkumi da ma sauran wasu batutuwan.
342/