1 Disamba 2021 - 14:15
Iran Ba Za Ta Sadaukar Da Hakkokin Alummarta Saboda Alkawulla Marasa Tabbaci Ba

Wani babban jami’in Iran a tattaunawar ta biyanna ya fadi cewa Iran ta shiga zagaye na 7 ne a ci gaba da tattaunawar da ake yi a biyanna da nufin sake farfado da yarjejeniyar nukiliya da aka cimma tsakanin Iran da sauran kasashen turai a shekara ta 2015 kuma bukatunta a fili suke karara kuma a shirye take ta gabatar idan da bukatar haka, sai dai ba za ta sadaukar da bukatu da hakkokin Alummarta ba saboda wa’adin na boge.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A ranar litinin da ta gabata ce wakilin Iran da na kasashen turai 5 wato Birtaniya Faransa Rasha China da kasar Jamus suka fara zama karo na 7 a birnin Biyanna fadar mulkin kasar Austiriya da zimmar farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran, ta JCPOA bayan dakatar da ita watanni 5 da suka gabata,

Daga karshe Iran ta bayyana cewa ba za ta amince da wani abu kasa da dauke dukkan takunkumin da Amurka ta kakaba mata ba, ba tare da wanu sharadi ba, kuma tana neman lamuni daga Amurka cewa ba za ta yi watsi da yarjejeniyar daga baya ba, kamar yadda Trumph yayi.

342/