27 Nuwamba 2021 - 12:02
​An Saki Tsoffin Jima’an gwamnatin Sudan Wadanda Ake Tsare Da Su Bayan Sun Fara Yajin CIn Abinci

An kara sakin wasu tsoffin jami’an gwamnatin kasar Sudan wadanda ake tsare da su tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 25 ga watan da ya gabata, kwana guda bayan sun fara yajin cin abinci.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa a safiyar yau ne aka bada labarin sakin Khalid Omar Yosif tsohon ministan al-amuran majalisar ministocin kasar da wasu da dama tare da shi.

Labarin ya kara da cewa a jiya ne wasu tsoffin ministoci da tsoffin jami’an gwamnatin kasar fararen hula suka fara yajin cin abinci don bukatar gwamnatin ta sake su daga tsarewar da take masu.

A ranar 25 ga watan Octoban da ya gabata ne Shugaban gwamnatin sojojin kasar ta Sudan Abdulfattah Burhan ya yiwa gwamnatin Abdulla Hamdok juyin mulk. Amma bayan shiga tsakani na wasu manya-manyan kasashen duniya sojojin sun sake maida Hamdok kan matsayinsa, da sharadin ya kafa sabuwar gwamnatin kwararru.

Labarin ya kara da cewa a safiyar yau ne sojojin suka saki Ayman Nimar tsohon gwamnan birnin Khartum. Har’ila yau a ranakun Jumma’a da litinin da suka gabata ma an saki wasu karin tsoffin jami’an gwamnatin da sojojin suke tsare da su.

342/