Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Kamfanin dillancin labaran Iran Press ko IP ya bayyana cewa manya-manyan jami’an tsaro na kasar Iran ne suka halarci bikin rufe gasar damben, daga ciki har da shugaban ‘yansada na kasa Burgediya Janar Hossain Ashtari wanda ya yaba da yadda jami’an ‘yansanda na kasar suka gudanar da gasar.
Labarin ya kara da cewa kasashen Rasha, Iran da kuma Armenia ne suka zo na farko, na biyu da na uku a gasar dambe wanda aka saba, sannan kasashen Iran, Rasha da Armenia ne suka zo na farko, na biyu da kuma na uku a damben gargajiyar irin na kasar Roma.
An raba lambobin yabo ga yan wasan da suka nuna bajinta a gasar, sannan Janar Jamshid Fuladi shugaban bangaren motsa jiki na sojojin kasar Iran ya bayyana cewa, gasar ta yi armashi saboda halattar fitattun ‘yan wasan dambe daga kasashen duniya da dama.
342/