16 Nuwamba 2021 - 19:03
Iran Ta Dora Alhakin Yanayin Da Ake Ciki Dangane Da Shirinta Na Makamashin Nukliya Kan Amurka

A wata tattaunawa ta wayar tarho da ministan harkokin wajen Iran Amir Abdallahiyan ya yi da takwaransa na kasar Italiya ya bayyana cewa dukkan bangarorin tattaunawa sun fahimci cewa Amurka ce da alhakin halin da ake ciki yanzu game da dawowar amurka cikin yarjejeniyar JCPOA na shirin nukiliyar kasar ta iran, saboda kin daukewa kasar takunkuman tattalin arzikin da ta kakabawa kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Ministan ya kara da cewa wasu bangarorin tattaunawar ba su yi aiki da nauyin da ya ratawa a wuyansu ba, ta yin shiru game da dagewar da Amurka ta ke yi wanda hakan ya taimaka sosai wajen tsawaita irin yanayin da ake ciki. Ya ce Iran tana aiki ne da cikawa.

Ana sa bangaren ministan harkokin wajen kasar Italiya Luigi Di Maio ya nuna aniyar kasarsa na kara fadada dangantaka tsakaninsu da Tehran, da kuma gamsuwarta game da matakan da ake dauka na ganin an gudanar da tattaunawar, ya kuma nuna fatansa na ganin an samu sakamako mai kyau da hakan zai taimaka wajen kara fadada dangantakar kasuwadci tsakanin kasashen biyu.

342/