15 Nuwamba 2021 - 17:01
​An Fara Zaman Gida A Kasar Austria Ga Wadanda Basu Yi Riga Kafin Cutar Covidi 19 Ba

Gwamnatin kasar Austria ta kafa dokar hana fita daga gida ga mutanen da basu yi alluran riga kafin cutar Covid 19 ba daga yau Litinin.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Kamfanin dillancin labaran Rauters ya nakalto wazirin kasar ta Austria Alexander Schallenberg yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa ya zama dole a dauki wannan matakin don yadda cutar take saurin yaduwa cikin wadanda suka rage basu yi riga kafin cutar ba.

Labarin ya kara da cewa a cikin duk mutane 100,000 a kasar mutun 815 ne suke kamuwa da cutar. Wannan duk da cewa kashi 65 % na mutanen kasar sun yi cikekken alluran riga kafin cutar.

Har’ila yau, yana daga cikin matakan da gwamnatin za ta dauka daga yau, wato hana duk wanda bai yi alluran riga kafin ba shiga gidajen cin abinci, filayen wasanni, gidajen cenima da wuraren jama’a, sai don sayan abinci ko kuma wata bukata ta musamman.

Banda haka duk wanda ya sabawar dokar fitan za’a ci shi tarar dalar Amurka $1,660. Sannan wannan halin zai ci gaba har na tsawon kwanaki 10 a duk fadin kasar.

342/