11 Nuwamba 2021 - 15:49
An Shiga Rudani A Libiya Gabanin Taron Kasa Da Kasa Kan Rikicin Kasar

An shiga rudani a Libiya, a daidai lokacin da kasashen duniya ke shirin gudanar da taro kan makomar kasar, kafin zaben ranar 24 ga watan Disamba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Yayin da babban zaben kasar ke katarowa, an samu sabani tsakanin wasu bangarori na kasar, da suka hada da firaministan kasar Abdel Hamid Dbeibah, da wasu ‘yan islama da kuma mayakan Tripoli, suka ki amincewa da dokar zaben kasar.

Khaled al-Meshri, shugaban majalisar koli mai bayar da shawara ga batun siyasar kasar Libya, ya yi kira ga masu kada kuri’a su kauracewa zabukan kasar dake tafe.

Yana mai cewa za’a koma ‘yar gidan jiya ne wato yaki, idan ba’a gusa zabubukan kasar ba.

al-Meshri, ya yi kira ga masu kada kuri’a su kauracewa zabukan kasar dake tafe.

Har ila yau, ya bayyana adawa da dokokin zaben da majalisar wakilan kasar ta gabatar, yana mai bayyana su a matsayin abun kunya.

Wasu bangarorin Libiyar dai na bukatar a gudanar da zaben raba gardama kan dokar zaben.

Sama da masu kada kuri’a miliyan 2.8 ne ake sa ran za su kada kuri’a domin zaben shugaban kasar a zaben ranar 24 ga watan Disamba.

342/