4 Nuwamba 2021 - 11:44
​Iran: Za’a Fara Taron Daukewa Iran Takunkuman Tattalin Arziki A Ranar 29 Ga Watan Nuwamba

Mataimakin ministan harkokin waje na kasar Iran Mohammad Bakiri ya bayyana cewa za’a fara taron tattauna yadda za’a daukewa kasarsa takunkuman zaluncin da Amurka ta dorawa kasar a birnin Vienna na kasar Austria a ranar 29 ga watan Nuwamba da muke ciki.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Bakiri yana fadar haka a shafinsa na Twitter a jiya Laraba. Ya kuma kara da cewa ya zanta ta wayar tarho da Enrique Mora jami’ii kungiyar tarayyar Turai mai kula da tattaunawar kafin a amince a sanya wannan ranar a matsayin ranar da za’a hadu don tattauna wannan batun.

Kungiyar tarayyar turai dai it ace mai shiga tsakanin a tattaunawar yarjejeniyar JCPOA wacce aka sanyawa hannu a shekara ta 2015, tare da samar da kudurin MDD mai lamba 2231 wanda yake tabbatar da yarjejeniyar. Amma a shekara ta 2018 shugaban kasar Amurka na lokacin Donal Trump ya fidda Amurka daga yarjejeniyar sannan ya maida dukkan takunkuman da aka dorawa iran kafin yarjejeniyan har da kara.

Iran kuma ta yi amfani da wani sashe na yarjejeniyar wanda ya bukace duk wata kasa da ta ga cewa daya ko sauran sun yi watsi da yarjejeniyar ita ma ta sake ta da nufin dawo da sauran kan ta.

342/