Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa Saudiya ta dauki wannan matakin ne bayan da ta bukaci ministan watsa labarai na kasar Lebanon George Kordahi ya nemi afwar gwamnatin kasar ta Saudiya kan furucinsa wanda ya aibata kasar a yakin da take fafatawa a kasar Yemen.
Banda haka gwamnatin kasar ta saudiya ta hana a sake shigo da wani kaya daga kasar Lebanon sai abinda hali yayi. Sannan ta gargadi yan kasar da su dakatar da tafiye-tafiye zuwa kasar Lebanon.
A makon da ya gabata ne ministan watsa labarai na kasar Lebanon George Kordahi ya yi kira ga gwamnatin kasar Saudiya ta kawo karshen yakin da take jagoranta a kan mutanen kasar Yemen tun shekara ta 2015.
342/