28 Oktoba 2021 - 15:21
Saudiyya Ta Saki Matashin Dan Shi’an Da Aka Yanke Wa Hukuncin Kisa

Hukumomin Saudiyya sun saki wani matashin dan Shi'a nan da ake tsare da a kurkuku, yau sama da shekara goma.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : An dai yanke wa Ali al-Nimr, hukuncin kisa yana da shekara 17, lamarin da lokacin ya janyo wa Saudiyya suka daga kungiyoyin kare hakkin dan adam na kasa da kasa.

Amma daga bisani an sauya masa hukuncin kisan da daurin shekara goma a gidan yari bayan da Saudiyya ta soke hukuncin kisa a kan yara a 2020.

Ali al-Nimr, wanda dan uwa ne ga shehun malamin shi’an nan na Saudiyya Ayatollah Al-Nimr, an kama shi ne a shekarar 2012 a kan shiga zanga-zangar kin jinin gwamnati a gabashin Saudiyya yankin da ya kunshi siraru ‘yan shi’a, aka kuma tuhume shi da laifukan da suka hada da mallakar makami da fashi da makami.

Zanga zangar waccen lokacin yayinta an kame ‘yan fafatuka na ‘yan shi’a da dama a yankin ciki har da Ayatollah Al’Nimir, wanda daga bisani Saudiyya ta zartar masa da hukuncin kisa ta hanyar hille masa kai a watan Janairu na 2016.

Zartar da hukuncin kan shehun malamim Al’Nimr, ya hadassa rikicin diflomatsiyya tsakanin Iran da Saudiyya.

342/