Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Bangarorin sun kira yajin aikin gama gari ne bayan juyin mulkin da sojoji sukayi a ranar Litini data gabata.
Al’amura sun tsaya cik a Khartoum babban birnin kasar sakamakon yajin aikin na masu adawa da juyin mulkin.
Ko a jiya Talata masu zanga zanga sun fito a sassa daban daban na kasar duk da katse intarnet da akayi.
Bayanai sun ce dawo da intarnet da yammacin jiya, saidai kuma daga bisani aka sake katse ta.
Rahotanni sun ce har yanzu sojoji na tsare da wurare masu mahimmanci musamman gewayen hedikwatar sojoji inda aka kashe masu zanga zanga a ranar Litini.
342/