Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Mali, na mai zargin jami’in da nuna halaye wadanda basa tafiya da matsayinta.
Wata sanarwa da gidan talabijin din kasar ya fitar da yammacin jiya, ta ce gwammnatin Mali ta dakatar da matsayin Hamidou Boly, wakilin kungiyar ta ECOWAS a kasar.
Malin, ta kuma baiwa jami’in sa’o’I 72 da ya tattara nasa ye nasa ya bar kasar.
Hukumomin Malin dai basu bayyana takamaimai halayen da ake zargin jami’in da aikatawa ba.
342/