25 Oktoba 2021 - 14:26
​Baje Kolin Kayayyakin Fasahohin Rubutu Na Musulunci A Ankara

Tun daga ranar sha biyu ga watan Rabiul Awwal aka fara gudanar da baje kolin kayayyakin fasahar rubutu da zane-zane na musulunci a birnin Ankara na Turkiya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A rahoton da kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar, tun daga ranar sha biyu ga watan Rabiul Awwal aka fara gudanar da baje kolin kayayyakin fasahar rubutu da zane-zane na musulunci a birnin Ankara na kasar Turkiya.

Wannan baje koli wanda karamin ofishin jakadancin Iran a kasar ta Turkiya ya dauki nauyin shiryawa, ya samu karbuwa matuka a wajen mutanen kasar da ma masu yawan bude ido a kasar.

A baje kolin dai ana nuna wasu daga cikin alluna da suke dauke da nau'oin ayyukan zane-zane na fasaha, da kuma rubutun ayoyin kur'ani ko addu'oi wadanda aka yi amfani da salo na musamman mai kayatarwa matuka wajen rubuta su.

342/