22 Oktoba 2021 - 16:09
Mali Ta Musanta Wakilta Wani Domin Tattaunawa Da ‘Yan Ta’adda

Gwamnatin Mali, ta musanta labarin cewa ta wakilta wani ko wasu domin tattaunawa da gungun kungiyoyi ‘yan ta’adda masu alaka da kungiyar Al-Qaïda.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Saidai gwamnatin Malin ta ce tana maraba da duk masu kyakyawar niyyar dake bukatar jagorantar tattaunawar.

A farkon makon majiyoyi da dama a Malin ciki har da daga ma’aikatar kula da addinai ta kasar da hukumar koli ta addinin islama a kasar sun tabbatar da cewa ana wannan tattaunawa.

A sanarwar data fitar gwamnatin Malin ta ce, babu kamshin gaskia game da hakan don kuwa babu wata kungiya ta kasa ko ta kasa da kasa da aka wakilta a hukumance domin yin irin wannan tattaunawar, kuma ita kanta gwamnatin kasar ta ce ta ji labarin ne ta hanyar kafofin yada labarai.

342/