20 Oktoba 2021 - 13:31
Uganda Ta Nuna Wata Motar Yaki Da Ta Kera

Shugaban kasar Uganda, Yoweri Museveni, ya kaddamar da bikin nuna wata motar soji da kasar ta kera.

Sunan motar Chui, wanda ke nufin Damisa a harshen Swahili.

Shugaban rundunonin sojin kasar, janar Muhoozi ya wallafa a shafinsa na tuwita wasu daga cikin hotunan motar da ya ce kirar gida ce.

Saidai bai bayyana abubuwan da ta motar ta kunsa ba ko kuma farashinta.

342/