9 Oktoba 2021 - 12:58
Amurka Na Ganawa Da Wakilan Taliban A Doha

A wannan Asabar ce ake sa ran wakilan gwamnatin Amurka dana Taliban zasuyi ganawar farko tun bayan da Amurka ta fice daga kasar Afghanistan.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : An tsara bangarorin zasu gana a birnin Doha na kasra Qatar, kamar yadda wani kakakin gwamnatin Amurka ya sanar.

Batun kare hakkin dan adam, da tattalin arziki da kuma taffafin jin kai, na daga cikin manyar ajandar tattaunawar.

Amurka ta ce zata matsa kaimi na ganin kungiyar Taliban dake mulkin Kabul, ta mutunta hakkin dukkan ‘yan Afghanistan musamman mata da yara, ta hanyar kafa gwamnatin data kunshi dukkan bangarori wacce kuma kowa zai aminta da ita.

Saidai Amurka ta sake nanata cewa wannan tattaunawar ba tana nufin ta amince da mulkin Taliban ba.

342/