8 Oktoba 2021 - 10:25
Iran Ta Yi Fatan Karfafa Alaka Da Japan A Fagage Da Dama

Shugaban kasar Iran, Ebrahim Ra’isi, ya yi fatan karfafa alaka tsakanin kasarsa da kuma Japon, a fagage da dama.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Wannan na kunshe ne a sakon da shugaba Ra’isi, ya aike wa sabon firaministan kasar ta Japan, Kishida Fumio.

A cikin wasikar shugaban kasra ta Iran, ya taya Mista Fumio, murna kan sabon mukamin nasa, ya kuma yi fatan kasashen biyu zasu karfafa alaka da kuma samar da ci gaba da zaman lafiya a yankin dama duniya baki daya.

Ya kuma yi fatan a wannan mukamin nasa sabon babi na mintaka zai bude tsakanin kasashen biyu, musamman ta fuskar tattalin arziki da kuma kasuwanci.

342/