8 Oktoba 2021 - 10:23
Abdollahian : Tattaunawar Rasha Da Iran Ta Yi Armashi

Ministan harkokin wajen kasra Iran, Hossein Amir-Abdollahian, ya bayyana tattaunawar da ta wakana tsakanin kasarsa da Rasha a matsayin mai cike da armashi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Ministan harkokin wajen kasar ta Iran, ya bayyana hakan ne bayan kammala ziyarar da ya kai Moscow inda ya gana da takwaransa, Sergio Lavrov.

Bangarorin sun tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi alakar dake tsakanin kasashen biyu.

Haka kuma sun tabo batutuwa da dama da suka shafi yankin dama duniya baki daya, musamman, Game da batun da ya shafi kasashen Afghanistan, Siriya, Caucas, Yemen da kuma yarjejeniyar nukiliyar Iran.

Sun kuma amince da yin aiki tare game da batutuwan da suka shafi yankin, da siyasa da tattalin arziki da kuma al’adu.

A wannan Alhamis dai ministan harkokin wajen kasar ta Iran, ya kuma isa binrin Beirut na kasra Labanon, inda ya tattauna da manyan jami’an kasar da dama ciki har da shuagba Michel Aoun.

342/