7 Oktoba 2021 - 11:15
​Guinea: Sabon Shugaban Kasar Ya Nada Beavogui A Matayin Sabon Firai Ministan Kasar

A Jiya Laraba ce sabon shugaban kasar Guinea Conakry ya nada Mohamed Beavogui, wani tsohon ma’aikin gwamnati a matsayin firai ministan rikon kwarya na kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : ya bayyana cewa Mohamed Beavogui, tsohon ma’aikin gwamnati ne kuma masanin ilmin ayyukan noma da kudade, zai jagoranci gwamnatin kasar ta Guinea zuwa lokacinda za’a gudanar da zabubbuka nan gaba, sannan a mayar da mulki ga fararen hula.

Banda haka Mohamed Beavogui dan shekara 68 a duniya, jikan Diallo Telli ne, tsohon jami’an diblomasiyyar kasar wanda ya taba zama shugaban kungiyar tarayyar Afika a baya, wanda kuma aka kashe a shekara 1977..

A ranar Jumma’an da ta gabata ce aka rantsar da kanar Mamadi Doumbouya a matsayin shugaban kasar Guinea na riko bayan juyin mulkin da ya jagoranta a ranar 5 ga watan satumban da ya gabata. Juyin mulki na kasar Guinea dai shi ne na 4 a kasashen yammacin Afirka bayan na Chadi da kasar Mali a baya bayan nan.

342/