5 Oktoba 2021 - 14:27
​Shugaban Kasar Tunisia Ya Ce Mutane Kimani Miliyon 1.8 Suka Fito Goyon Bayansa

Shugaban kasar Tunisia Kais Saed ya ce mutane kimani miliyon 1.8 suka fito don nuna goyon bayansa a ranar Lahadin da ta gabata.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Shugaban ya bayyana haka ne a lokacinda yake ganawa da sabuwar firai ministan kasar da ya nada, ya kuma kara da cewa mutanen kasar Tunisia sun yi magana kuma ba zai kunyatasu ba. Don haka zai ci gaba da shirye-shiryen da yake da su na gabatar da sauye sauyen a tsarin mulki na kasar Tunisia.

Kafin haka dai magoya bayan ‘yan adawa sun fito zanga zangar yin allawadai da shirin shugaban kasar na gabatar da sauye sauye a kundin tsarin mulkin kasar.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya ce a ganinsa mutanen da suka fito goyon bayan shugaban kasar basu fi 8000.

342/