Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Shugaban majalisar koli ta kungiyar Sayyid Hashim Safi’uddin ya bayyana haka a jiya da yamma a wani taron da ya halatta a garin Bint-Jbeil daga kudancin kasar.
Safi’uddin ya kara da cewa, ya san cewa mutanen kasar Lebanon suna jin tsoron manya manyan kasashen duniya, amma shigo da makamashi daga kasar Iran ya bayyana gazawar haramtacciyar kasar Isra’ila wajen hana makashin isa kasar Lenakon daga kasar Iran.
Ya kuma kara da cewa duk wani zabin da kasar Lebanon zata yi ba ta nuna diyauci ba, mika kai ne ga bukatun HKI a yankin. Don haka banda shigo da makamashi daga kasar Iran akwai wasu shirye-shiryen wanda kungiyar take da su don tabbatar da diyaucin kasar Lebanon da kuma fidda ita daga mummunan halin da aka jefata ciki.
342/