Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Duk da cewa ba’a fitar da bayyanan tattaunawar ba, amma bayanai sun ce shugaba Erdogan ya je ne domin tattauna yadda kasashen zasu karfafa alakar dake a tsakaninsu.
Turkiyya da Rasha, kawayen june ne saidai suna da sabani akan wasu batutuwa musamman kan batun yankin Idlib na kasar Siriya.
Shugaba Putin, ya bayyana cewa ‘’a wasu lokutan ba’a samun sauki a tattaunawa, amma daga karshe akan samu mafita’’ inda kuma ya yaba da matsayar da kasashen biyu suka cimma.
Shi kuwa shugaban kasar ta Turkiyya, cewa ya yi akwai babbar riba, ya kasance cewa kasashen Rasha da Turkiyya, sun ci gaba da karfafa alakar dake a tsakaninsu.
Akan sha’anin tsaro kuma babu wani bayyani da ya fito kan batun ci gaba da sayar wa da Turkiyya makamman garkuwa game da hare haren sama S-400 kirar kasar Rasha.
Saidai an ce Rasha na kara matsin lamba wajen neman sayar wa da Turkiyya jiragen yaki kirar Sukhoi Su-35.
342/