30 Satumba 2021 - 13:15
Kasar Iraqi Za Ta Sayi Garkuwan Tsaron Sararin Samaniya Samfarin S-300 Daga Kasar Rasha.

Babban kwamandan sojojin sama na Kasar Iraki Janaral Shihab Jahid Ali da ya jagoranci wata tawaga zuwa kasar Rasha a bayan bayan nan, ya fadi cewa sun kulla yarjejeniya game da seyan Na’aurar tsaron sararin samaniya samfarin S-300 daga kasar Rasha domin kara karfin tsaronta yadda za ta iya kare kasar daga duk wani wuce gona da iri.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A shekarar da ta gabata wani dan majalisar kasar iraki ya fadi cewa Amurka tana nuna adawa da sayan Na’urar bada kariya ta sararin samaniya samfarin S -400 daga kasar Rasha ne saboda fargabar da take da shi na rage karfinta da kuma kashe mata kasuwar makami a yankin gabas ta tsakiya.

Ana sa bangaren Mohammad Albadawi mamba a kwamitin tsaro na majalisar kasar Iraki ya fadi cewa Babban dalilin da ya sa Amurka ke kokarin kange kasar Rasha daga sayar da makaman kariya na sararin samaniya ga kasashen Iraki, yankin tekun fasha ko Iran ko kuma wata kasa a yankin gabas ta tsakiya saboda kasar Amurka da isra’ila za su rasa ikon da suke da shi a sararin samaniyar kasashen yanki da kuma yanci amfani da sararin samaniyar kasashen wajen kai hari kan kasashen dake adawa da Isra’ila..

342/