Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Daruruwan masu zanga -zanga sun yi gangami a babban birnin kasar ranar Lahadi, don nuna adawa da matakin Shugaba Kais Saied na mamaye ikon gwamnatin kasar baki daya.
Zanga -zangar dai ita ce ta biyu tun lokacin da shugaba Saied ya dakatar da majalisar dokokin kasar a ranar 25 ga Yuli, kafin daga bisani ya kori Firaministansa kana kuma ya nada kansa a matsayin mai gabatar da kara.
An gudanar da zanga zangar cikin tsauraren matakan tsaro, domin dakile barazanar aukuwar kazamin bore.
Kimanin kungiyoyin kare hakkin dan adam na kasa da kasa da na Tunisia 20 ne suka yi tir da matakin na shugaba Kais Saed.
342/