Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa wannan shi ne zanga-zanga mafi girma wanda aka yi tun bayan da shugaban kasar ya kori firai minista ya rufe majalisar dokokin kasar sannan ya bawa kansa cikekken iko kan al-amuran shugabancin kasar.
Masu zanga-zangar dai sun ce shugaban ya yi watsi da kundin tsarin mulkin kasar, kuma suna adawa da duk wani sauyin da zai yi masa.
Cin hanci da rashawa da rikice-rikicen siyasa sun yi yawa a tsakanin ‘yan siyasa masu iko da kasar Tunisia kafin shugaban ya dau wannan mataki mai tsauri da kuma kaddamar da shirin sauya tsarin shugabnci a kasar.
‘Yansanda sun yi dafifi kan a kan titin Bogiba a tsakiyar birnin Tunisia don hana wuce gona da iri tsakanin magoya da masu adawa da shugaba Kais Sa’id.
342/