25 Satumba 2021 - 14:35
An Kafa Sabuwar Majalisar Rikon Kwarya A Chadi

Shugaban gwamnatin sojan Chadi, Mahamat Idriss Deby Itno ya bayyana mambobi 93 na sabuwar majalisar rikon kwaryar kasar, watanni biyar bayan ayyana kansa a matsayin shugaba, sakamakon rasuwar mahaifinsa Idriss Deby Itno.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Idan za a tuna a ranar 20 ga Afrilu, Mahamat Idriss Deby ya rusa majalisar Chadi tare da yin alkawarin shirya zabe cikin watanni 18, bayan ayyana kansa a matsayin sabon shugaba.

Akwai dai masu adawa da tsohon shugaba Deby cikin membobin majalisar dokokin rikon kwaryar ta Chadi, sai dai babu mamba ko guda daga cikin kungiyar ‘yan adawa ta Wakit Tamma, ko kuma daga kungiyoyin farar hula da basu goyi bayan kama mulkin dan Idriss Deby ba.

Ranar 11 ga watan Mayu, gwamnatin sojin Chadi ta nada tsohon firaministan kasar Albert Pahimi, kan tsohon mukamin nasa amma na rikon kwarya.

342/