18 Satumba 2021 - 10:04
Bukatar Da Sayyid Hassan Nasrullah Ke Da Ita Ga Al'ummar Lebanon

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya yi kira ga al'ummar Labanon da kada su gudanar da wani gangami don saukin isowar ayarin tankokin mai zuwa Lebanon.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti (AS) -ABNA ya ruwaito, "Sayyid Hassan Nasrallah", babban sakataren kungiyar Hizbullah a Lebanon, a jajibirin isar da tankokin mai na Iran zuwa Lebanon, ya godewa jama'a tare da rokon su kan cigaba da kiyaye kiwon lafiya da sauƙaƙe isowar ayarin mai zuwa Lebanon da kada su gudanar da wani gangami.

Tun da farko a cikin jawabinsa a daren Litinin, ya sanar da isowar tankokin man Iran na farko a yankin Bekaa, yana mai cewa jirgin ruwan na Iran ya isa tashar jiragen ruwa ta Banias ta Siriya a daren Lahadin kuma jigilar farko na man Iran zai shiga cikin Yankin Bekaa a ranar Alhamis.

Babban sakataren kungiyar ta Hizbullah ya kuma ce game da inda tankokin mai na Iran suka nufa da cewa akwai zabi biyu ga inda jirgin farko zai dosa; na farko zai sauke kayansa a Lebanon ko sauke kayansa a Siriya.

Yace "Hizbullah ta yanke shawarar tura tankar mai zuwa Siriya saboda kar wasu bangarori su kasance cikin tsaka mai wuya.
Da yake sanar da isowar tankokin mai daga tashar jiragen ruwa na Banias zuwa Ba'albek ta Lebanon, Ahmad Ria, jami'in watsa labarai na Hezbollah a Al-Baqa, ya ce tankar za ta isa Ba'albek ranar Alhamis.

342/