15 Satumba 2021 - 11:29
​Ra’isi Da Putin Sun Tattauna Hayoyin Kara Bunkasa Alakoki Tsakanin Iran Da Rasha

Shugabannin kasashen Iran da Rasha sun gudanar da wata tattaunawa ta wayar tarho kan yadda za su kara bunkasa alakokinsu kasashensu a dukkanin bangarori.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tashar PressTV ta bayar da rahoton cewa, a yayin tattaunawar wadda ta gudana a yammacin tsakanin shugaba Ibrahim Ra’isi na Iran, da kuma shugaba Vladimir Putin na Rasha, bangarorin biyu sun tattauna batutuwa da dama da suka shafi alaka tsakanin kasashensu.

Shugaba Ra’isi ya sheda wa Putin cewa, kyakkyawar alakar da ke tsakanin Iran da Rasha abin buga misali ce, kamar yadda kuma dukkanin bangarorin biyu suke yin aiki tare a bangarori daban-daban domin ci gaban al’ummominsu.

Shi ma a nasa bangaren shugaba Putin ya jaddada matsayin gwamnatin Rasha na ci gaba da yin aiki tare da Iran kafada da kafada a dukkanin bangarori nasiyasa, tattalin arziki, tsaro, cinikayya, bincike na ilimi da sauransu.

Kasashen Rasha da Iran dai suna da kyakkayawar alaka a dukkanin bangarori, kamar yadda kuma suke gudanar da ayyuka a bangaren nukiliya, inda Rasha ta taka gagarumar rawa wajen taimaka ma Iran a shirinta na nukiliya.

342/