8 Satumba 2021 - 13:43
​ECOWAS Bata Gamsu Da Shirye-Shiryen Zabuka A Mali Ba

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin afirka ECOWAS ta bayyana cewa shirye-shiryen gudanar da zabubbuka a shekara mai zuwa a kasar Mali bai gamsar da ita ba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : ya bayyana cewa kungiyar ECOWAS ta na sanya ido kan yadda shirye-shiryen zabubbuka suke tafiya a kasar ta Mali bayan wani juyin mulkin da sojoji suka yi a shekarar da ta gabata.

Labarin ya kara da cewa har yanzun ba’a bayya ranakun zabubbuka, da kuma rijistar sunayen masu zabe a cikin watan Fabrairun na shekara mai zuwa ba.

A jiya talace tawagar kungiyar karkashin jagorancin tsohon shugaban tarayyar Najeriya Mr Goodluck Jonathan ta kai ziyara zuwa kasar ta Mali don ganewa idanunta irin ci gaban da aka samu a wannan bangaren.

Jami’an gwamnatin kasar ta Mali dai, sun bayyana cewa suna sane da abinda ya hau kansu, kuma suna aiki don ganin an gudanar da zabubbuka a cikin watan Fabrairu na shekara ta 2022 kamar yadda aka tsara.

342/