8 Satumba 2021 - 13:39
Taliban Ta Sanar Da Kafa Sabuwar Gwamnati A Afghanistan

Kungiyar Taliban a Afghanistan ta sanar da kafa sabuwar gwamnati a wannan Talata.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Kakakin kungiyar ne Zabihullah Mujahid ya sanar da mambobin sabuwar gwamnatin da ministoci daban-daban, makonni uku bayan kwace mulki daga hannun gwamnatin Kabul.

Mullah Muhammad Hassan Akhund, daya daga cikin wandanda suka kafa kungiyar, an nada shi a mukamin Firaminista na Afghanistan.

An nada Mullah Abdul Ghani Baradar a matsayin Mataimakin fira minista.

Sauren mambobin sabuwar gwamnatin da aka sanar da nadin nasu, sun hada da Sarrajuddin Haqqani wanda zai zama ministan harkokin cikin gida, sai Mullah Yaqoob zai zama ministan tsaro, yayin da Abas Stanikzai kuma zai zama mukadashin ministan harkokin waje.

342/